logo

HAUSA

Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya gana da shugabannin kungiyoyin addinin musuluncin kasar

2023-03-26 15:45:21 CMG Hausa

Shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya gana da manya manyan shugabannin kungiyoyin addinin musuluncin kasar a ranar Jumma’a da ta gabata a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai, ganawar da ta zo daidai lokacin watan azumin shekarar 2023 da muke ciki a kasar Nijar da ma sauran wasu kasashen musulunci na duniya.

Daga birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, wakilin mu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Ita dai wannan ganawa da shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke nan birnin Yamai, na da muhimmancin gaske. Shugaba Bazoum ya bukaci kungiyoyin addinin musulunci na kasa baki daya da su yi amfani da wannan dama ta watan azumi mai cike da falala da daraja, ta hanyar gudanar da salloli da karatun Alkur’ani mai tsarki a cikin masallatai, domin rokon Allah alherin da ke cikin watan Ramadan domin neman gafara, tsaro, zaman lafiya da kariyar sojojinmu da ke fagen daga da kuma neman cigaban kasarmu, in ji Ibrahim Seyni, kakakin wadannan kungiyoyin addinin musulunci.

Mai magana da yawun kungiyoyin addinin musulunci na kasa ya ce, sun dauki niyyar yin kira da babbar murya ga musulman Nijar da tashi tsaye zuwa ga rokon Allah wata baraka.

A yayin wannan ganawa ta keke da keke, shugabannin kungiyoyin musuluncin sun gabatarwa shugaban kasa matsalolinsu da na al’ummar musulmin, musammun ma batun ilimin kananan yara a cikin kasa da dai sauran batutuwan da suka jibanci tarbiya da tabarbarewar al’adu, a cewar Ibrahim Seyni. Inda ya kara da cewa, shugabannin addinin musulunci da suka halarci wannan haduwa, sun bukaci shugaban kasa da gwamnatinsa da su duba batun sanya hannun jari ga kowane mahajjacin Nijar daga gwamnati domin rage masa kashin kudi na aikin hajji da umra, ganin cewa a kowace shekara kudin kujera zuwa kasar Saudiyya na karuwa. (Mamane Ada)