logo

HAUSA

Gyare-gyare su kan faru ne bisa sauyawar tunanin mutum

2023-03-23 20:48:57 CMG Hausa

Abokaina, a kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kai ziyara kasar Rasha, inda ya gana da takwaransa na kasar Vladimir Putin. Dangane da wannan batu, wane irin ra’ayi su kasashen yamma za su dauka, wannan ba sai na fada ba, ku ma za ku sani. Sai dai a nan za mu kyale ra’ayinsu, domin ina so in nuna muku wasu ra’ayoyi daga ‘yan Afirka.

An gudanar da wani taro mai taken “ Dimokuradiya: tunani mai daraja na daukacin dan Adam” a birnin Beijing na kasar Sin a kwanan nan, inda na samu damar tattauna da wasu masana da ‘yan siyasa na kasashen Afirka wadanda suka halarci taron, kuma na tambaye su kan ra’ayinsu dangane da ziyarar shugaba Xi a wannan karo. Sa’an nan Mista Charles Onunaiju, shehun malami mai nazarin harkoki masu alaka da kasar Sin na Najeriya, ya gaya mana cewa, hadin gwiwar kasashen Sin da Rasha ta sa ake samun daidaituwa a duniya, wadda ke taimakawa samar da wani yanayi na kwanciyar hankali. Ya ce idan babu hadin kan Sin da Rasha, za a samu karin juyin mulki, da tashin hankali, da rushewar tattalin arziki a wurare daban daban, sakamakon yadda wasu kasashen yamma suke cin kare babu babaka.

A nashi bangaren, shugaban jam’iyyar Socialist ta kasar Zambia, Dokta Fred M’membe, ya ce, shugabannin kasashen Sin da Rasha suna kokarin jagorantar aikin neman samun karin bangarori masu fada a ji a duniya. Ta yin la’akari da yadda dimbin kasashe irinsu India, da Brazil su ma suke shiga a dama da su, ana iya cewa, ba za a iya hana irin yanayi na samun karin bangarori masu tasiri a duniya ba.

Ban da haka, Kugiza Kaheru, mamban kwamitin kare hakkin dan Adam na kasar Uganda, ya gaya mana cewa, “Shugaba Xi Jinping yana neman ganin an daidaita rikicin da ake samu tsakanin Rasha da Ukraine ta hanyar sulhu. Wannan buri ne mai kyau, ya kamata a goyi bayansa, maimakon daukar matakai na soja.”

Wadannan mutane sun zo daga yammaci da gabashin Afirka, wadanda suka kasance masana ko kuma ‘yan siyasa. Sai dai dukkansu sun nuna goyon baya ga yadda ake yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Rasha, da kokarin kasar Sin na neman tabbatar da zaman lafiya.

Bayan mun tattauna ra’ayi na ‘yan Afirka, bari mu duba ainihin sakamakon da aka samu daga ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Rasha. Bisa labaran da aka watsa, da farko dai, ban da sanar da burin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Rasha, shugabannin 2 sun yi alkawarin aiwatar da ra’ayi na kasancewar bangarori masu fada a ji da yawa a duniya, da tabbatar da dimokuradiyya yayin da ake gudanar da harkokin kasa da kasa, ta yadda za a samar da karin gudunmowa ga aikin neman ci gaban al’ummar dan Adam.

Na biyu, shi ne shugabannin 2 sun sa hannu kan wata hadaddiyar sanarwa, inda suka jaddada bukatar daidaita rikicin kasar Ukraine ta hanyar yin shawarwari. A hakika, wadannan sakamakon da aka samu sun zama daya da hasashen da masana da ‘yan siyasa na kasashen Afirka suka yi.

Sa’an nan idan mun kwatanta ra’ayi na wasu ‘yan Afirka wanda muka ambata a baya, da hakikanin abun da ke faruwa, muna iya gano cewa, Afirka ta riga ta canza, inda kasashen yamma, tsoffin ‘yan mulkin mallaka, suka fara rasa damar yin tasiri kan tunanin mutanen kasashen Afirka. Yanzu masana da ‘yan siyasa na kasashen Afirka suna iya yin tunani kan harkokin kasa da kasa yadda ake bukata, don kare moriyar kasashen Afirka, da fahimtar gaskiyar abubuwa.

Ana samun sauyawar yanayi, ko da yake kafofin watsa labaru na kasashen Afirka na ci gaba da yin amfani da bayanan da takwarorinsu na kasashen yamma suka hada, kana ana samun cacar baki a kasashen Afirka, tsakanin masu goyon bayan kasashen yamma, da wadanda suke kin amincewa da su.

Dangane da sauyawar yanayin da ake samu, ina so in ambaci wani misali na daban: A kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da shawarar wayewar kai ta duniya, inda ya yi kira da a girmama yanayi na samun mabambantan wayewar kai a duniya, da amince da zabin kasa da kasa na neman wata dabara mai kima ta raya kansu. Wannan shawara ta samu goyon baya sosai daga masana, da ‘yan siyasa na kasashen Afirka, wadanda a wajen taron “ Dimokuradiya: tunani mai daraja na daukacin dan Adam”, suka tsaya kan cewar, babu wani daidaitaccen tsarin dimokuradiya daya tilo. Hakika ya kamata a lura da tarihi na wata kasa, da kokarin biyan bukatar kasar wajen daidaita matsalolinta, da lura da halayyar musamman ta wata kasa, da karfafa fahimtar juna, da hadin kai, tsakanin al’ummu daban daban, yayin da ake raya harkar dimokuradiya a wata kasa. Kar a ba wasu kasashen damar shawo kan sauran kasashe, ta fakewa da maganar dimokuradiya.

Yadda ake samun ra’ayi na bai daya tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, ya nuna cewa ra’ayi na mai da kasashen yamma cibiyar duniya ya zama tsohon yayi, yayin da karin kasashe masu tasowa ke neman tabbatar da tsarin dimokuradiya a duniya, da kasancewar mabambantan tunani game da al’adu da siyasa a kasashe daban daban, bisa bukatarsu ta raya kansu.

Gyare-gyare su kan faru ne bisa samun sauyawar tunanin mutum. Idan kun yarda da ni, wajen ganin rashin dimokuradiyya, da adalci, a harkokin kasa da kasa, to, sauyawar yanayin da ake samu yanzu shi ne ainihin abun da muke bukata. (Bello Wang)