logo

HAUSA

Me ya sa Amurka ta sake rura wuta kan batun gano asalin annobar Covid-19?

2023-03-22 22:02:31 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Kwanan nan, gwamnatin kasar Amurka ta sake rura wuta kan batun gano asalin annobar Covid-19, inda bi da bi, ma’aikatar makamashi ta kasar da hukumar bincike ta FBI suka bayyana cewa, “Ta yiwu” annobar ta samo asalinta ne daga dakin gwaji na kasar Sin, sai kuma majalisun dokokin kasar suka zartas da shirin doka, da ya shafi batun gano asalin annobar, wanda kuma shugaba Biden na Amurkar ya sa hannu a kansa don ya zama doka.

Duk da cewa, gano asalin cutar nauyi ne na bai daya dake wuyan kasa da kasa, amma akwai shakku game da yadda Amurkar ke “gano asalinta”. Na farko, gano asalin cutar aiki ne da ya shafi kimiyya, wanda ya kamata a dorawa masana ilimin kimiyya na kasa da kasa, amma me ya sa Amurkar ta dora aikin a wuyan sassan kula da makamashi da na leken asiri? Na biyu kuwa, me ya sa Amurka ta yi ta yayata karairayi game da wai “cutar na daga dakin gwaji” tare da nuna yatsa ga kasar Sin, amma ba tare da samar da shaidu ba? Lallai, ta hakan muna iya ganin yadda take siyasantar da cutar, a kokarin cimma burinta na shafa wa kasar Sin kashin kaza.

Hasali ma dai, Amurka ta saba da daukar irin wannan mataki don cimma burinta. Idan ba a manta ba, yau shekaru 20 da suka wuce, ta zargi kasar Iraki da mallakar makaman kare dangi, kuma da wannan hujja ce ta kaddamar da yaki a kasar, amma ga shi har yanzu ta kasa samar da shaidu kan hakan, duk da haka Iraki ta lalace sakamakon yakin. Ga kuma abin da ta aikata a Syria da ma a kan batun bututun iskar gas na “Nord Stream”, hakika abubuwan da ta yi sun wuce zaton al’umma.

A cikin ‘yan shekarun baya, Amurka ta dauki duk matakan da ta ga dama don dakile kasar Sin, da haka muke iya fahimtar me ya sa take sake rura wuta a kan batun gano asalin cutar. A hakika, wannan daya ne daga cikin jerin matakanta na kalubalantar kasar Sin.

Sama da shekaru uku ke nan bayan aukuwar annobar Covid-19, kuma kasashen duniya na farfadowa daga barnar da annobar ta haifar.  Annobar ta kuma sake shaida mana cewa, a gaban mummunar matsalar da ta shafi duniya baki daya, kasa da kasa na cikin babban jirgi daya ne a maimakon kowanensu na cikin karamin jirgi daya tilo, kuma babban jirgin na iya tinkarar guguwa mai karfi a maimakon karamin jirgi.

Har kullum, kasar Sin na goyon baya tare da sa hannu a aikin gano asalin cutar da aka gudanar a kimiyyance, amma kuma tana adawa da siyasantar da cutar ta ko wace hanya. Jirgi daya ne ‘Yan Adam suke ciki, don haka, ya kamata su hada gwiwa da juna a maimakon yin fito na fito, ta hakan kuma suke iya isa inda suka dosa. Kamata ya yi Amurka ta yi watsi da ra’ayin cacar baka, ta hada kai da kasar Sin da ma sauran kasashen duniya baki daya, don ta taka rawar da ta dace da matsayinta, a fannonin gano asalin cutar, da farfado da tattalin arzikin duniya da ma gudanar da harkokin duniya. (Mai zane: Mustapha Bulama)