logo

HAUSA

93.15% na mutanen da aka ji ra’ayinsu a duniya sun nemi Amurka da ta dauki alhakin aikata laifin yaki

2023-03-20 15:12:43 CMG HAUSA

 

Yau 20 ga watan nan na Maris, rana ce ta cika shekaru 20, tun bayan da Amurka ta kaddamar da kai hari kasar Iraki. Bisa wani nazarin jin ra’ayin jama’ar duniya da CGTN ta gudanar, laso 93.15% daga cikin mutanen da suka bayyana ra’ayinsu game da wannan yaki, sun nuna cewa, ya kamata Amurka ta dauki alhakin aiwatar da laifin yaki a Iraki.

A cikin shekaru 20 da suka gabata, Amurka da kawayenta, sun kaiwa Iraki hari ba tare da samun izini daga MMD ba, bisa hujjar cewa, ta gano makaman kare-dangi a Iraki. Daga baya, an tabbatar da cewa, Iraki ba ta da irin wadannan makamai. Ya zuwa yanzu, kaso 94.6% na yawan mutanen da aka ji ra’ayinsu na ganin cewa, babu wani dalilin da ya dace Amurka ta kaddamar da wannan yaki a Iraki, kuma yin hakan laifi ne.  

A cikin wadannan shekaru 20 da suka gabata, yawan fararen hula da suka mutu, ko suka jikkata, ya kai fiye da dubu 200, yayin da wasu miliyoyin mutanen sun rasa gidajensu. A na su bangare kuwa, sojojin Amurka 4,572 sun mutu, kana yawan kudin da kasar ta kashe ya kai fiye da dala triliyan 2. Kaiwa Iraki hari da Amurka ta yi, ko shakka babu, laifi da gwamnatin Amurkan ta aikata.  (Amina Xu)