logo

HAUSA

Kashi 93.15 cikin 100 na wadanda aka zanta da sun bunkaci Amurka da ta yi la’akari da laifukan yakin da take aikatawa

2023-03-19 16:29:23 CMG Hausa

Ranar Litinin 20 ga watan Maris ne, ake cika shekaru 20 da Amurka ta kaddamar da yaki a kasar Iraki.  A cewar wani binciken kuri’ar jin ra’ayin jama’a kan masu amfani da Intanet a duniya da CGTN ta gudanar ta nuna cewa, kashi 93.15 cikin 100 na wadanda aka zanta da su sun yi imanin cewa, ya kamata Amurka ta dauki alhakin laifukan yaki da ta aikata a kasar Iraki.

Shekaru 20 da suka gabata, Amurka da kawayenta sun yi ikirarin cewa, akwai tarin makaman kare dangi da aka boye a kasar ta Iraki, inda suka kai mata hari ba bisa ka’ida ba, ba kuma tare da iznin MDD ba. Sai dai kuma daga bisani an tabbatar da cewa, abin da ake kira wai "makaman kare dangi" da ake ta batu a kai karya ne kawai. Bugu da kari, kashi 94.6 cikin 100 na wadanda aka ji ra’ayoyinsu a duniya sun yi imanin cewa, babu wata hujja da zai sa Amurka ta kaddamar da yaki a kasar ta Iraki. Wannan ba daidai ba ne.

A cikin shekaru 20 din, an tabbatar da cewa, abin da ake kira "tsarin demokradiyya" na Amurka bai kawo 'yanci da zaman lafiya a kasar Iraki ba, kamar yadda gwamnatin Amurka ta yi alkawari. A maimakon haka ma, tsarin ya haifar da rushewar tsarin da ya gabata, an kuma fuskanci ayyukan ta'addanci ba kakkautawa, da mummunar rarrabuwar kawuna da asarar rayuwa ga talakawa da dama. Kimanin kashi 94.56 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, demokuradiyya irin ta Amurka, ba za ta iya kawo 'yanci na hakika ga duniya ba.

An kaddamar da binciken kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ne a kafafen yada labarai na CGTN na Turanci da Sifaniyanci da Faransa da Larabci da Rashanci, inda sama da mutane dubu 80 suka kada kuri’a cikin sa’o’i 24. (Ibrahim)