logo

HAUSA

Seymour Hersh ya sake rubuta sharhi kan fasa bututun “Nord Stream”

2023-03-19 16:04:14 CMG Hausa

Seymour Hersh, wani dan jarida ne na kasar Amurka wanda ya taba rubuta labarin a watan Fabrairun wannan shekara, inda ya bayyana cewa, Amurka ce ta shirya fasa bututun jigilar iskar gas na “Nord Stream”, kwanan nan ya sake wallafa wani labarin dake nuna cewa, abin da ke tattare da harin bam din shi ne halin Amurka a ko da yaushe na nunawa saura ra’ayinta fin karfi da yaji.

Hersh ya bayyana a cikin sharhin nasa cewa, shekaru da yawa, gwamnatocin Amurka da dama sun yi amfani da matakan matsin lamba kamar takunkumi don hana samar da makamashin Rasha zuwa Turai.

Tun a shekarar 2014, lokacin da yake rike da mataimakin shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya yi gargadin cewa, dole ne Rasha ta martaba dokokin Amurka. Wannan shi ya haifar da tayar da bam kan bututun “Nord Stream” bayan shekaru takwas. Bayan da Biden ya zama shugaban kasa, ya yi watsi da muradun kawancen Turai, ya kuma amince da lalata bututun "Nord Stream" a bara. Amma mai yiwuwa ne Biden da tawagarsa ba za su amince da abin da suka aikata ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)