logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya yi fatan sabuwar gwamnatin kasar za ta dora wajen yaki da cin hanci a tsakanin ma’aikata

2023-03-17 09:18:18 CMG Hausa

A ranar alAhamis 16 ga wata, shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi fatan sabuwar gwamnatin kasar mai zuwa za ta dora daga inda ya tsaya wajen yaki da cin hanci da rashawa a ma’aikatun gwamnati. 

Shugaban ya bukaci hakan ne a fadarsa dake birnin Abuja lokacin da ya gudanar da wani taro da shugabannin kotun da’ar ma’aikata ta kasar karkashin jagorancin shugaban ta Danladi Umar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaban Muhammadu Buhari ya ce babban abun da yake saurin hana ci gaban kowacce gwamnati shi ne cin hanci da yake yin katutu a tsakanin ma’aikatan.

Ya ce nasarar da gwamnatinsa ta samu wajen yaki da cin hanci a tsawon shekaru 7 ya dogaro ne da irin gudumawar da kotun ta bayar, a don haka zai yi kyau shugaban kasa mai jiran gado ya yi tafiya da kotun da hannu bibbiyu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ci gaba da cewa duk da kalubalen tattalin arziki da koma bayan kudaden shiga a kasar, kotun da’ar ma’aikatan ta yi rawar gani sosai wajen ceto Najeriya daga shiga wani hali mawuyaci, ko da yake har yanzu Najeriya na fuskantar barazana daga wasu bara gurbin ma’aikata da ake damkawa amanar dukiyar jama’a.

Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa tabbatar da da’a a a tsakanin ma’aikaci babban jihadi ne da zai kara dora kowace kasa kan turbar kyakkyawa da za ta kara fito da darajar gwamnatoci a dukkan matakai.

A sabo da haka shugaba Buhari ya kira ga shugabannin kotun da su ci gaba da gudanar da aikinsu ba tare da nuna wani son zuciya ba, sannan kuma su kasance masu kokarin bin dokokkin dake da nasaba da ayyukan kotun.

Da yake jawabi, shugaban kotun da’ar ma’aikatan ta tarayyar Najeriya Alhaji Danladi Umar yabawa shugaban kasar ya yi bisa irin nasarorin da gwamatinsa ta samu a tsawon shekarun mulkinsa ta fuskar samar da ababen ci gaba, aikin gona da sauran fannoni na ci gaban al’umma.

Ko da yake shugaban kotun da’ar ma’aikatan ya koka a fannin kalubalen karancin kudi da kotun ke fuskanta, da kuma rashin wadatattun ma’aikata, a don haka ya bukaci agajin shugaban kasar.

Ya kuma yi alkawarin cewa ma’aikatan kotun za su ci gaba da gudanar da aikinsu bisa gaskiya da adalci tare da la’akari da dokokin da suka samar da kotun.

An dai samar da kotun ne a 1979 karkashin mulkin farar hula na wancan lokaci bayan karewar shekaru 13 na mulkin soja. 

Daga cikin ayyukan ita wannan kotun sun hada da bibbiyar kaddarorin masu rike da mukaman gwamnati, da kuma wadanda ake kokarin baiwa wani mukami a gwamnatoci domin tabbatar da ganin an rage yawan rub da ciki kan dukiyoyin al’umma. (Garba Abdullahi Bagwai)