logo

HAUSA

Me ya sa kasar Sin za ta kafa tashar nazarin kimiyya a duniyar Wata?

2024-04-25 18:51:44 CMG Hausa

Masu kallonmu, barka da war haka. Za a harba kumbon Shenzhou-18 mai dauke da ‘yan sama jannati a daren yau Alhamis, da karfe 9 saura minti daya agogon birnin Beijing. Baya ga ci gaban da Sin ta samu a fannin harba kumbo mai dauke da mutane zuwa sararin samaniya, tana kuma gudanar da shirin harba kumbo mai dauke da mutane zuwa duniyar Wata kamar yadda take fata. Jiya hukumar lura da binciken sararin samaniya ta Sin ko CNSA ta gabatar da wani bidiyo dangane da yadda za ta kafa tashar nazarin kimiyya ta kasa da kasa a duniyar Wata. To, me ya sa za a kafa tashar? Bari mu duba tare.