logo

HAUSA

Sin ta shawarci WTO da ta tattauna matakan kiyaye muhalli tsakanin bangarori daban-daban

2023-03-16 20:35:41 CMG HAUSA

 

A jiya Laraba ne, kasar Sin ta shawarci kungiyar ciniki ta duniya ta WTO da ta zurfafa mu’ammala kan matakan kiyaye muhalli tsakanin bangarorin daban-daban.

Mambobin kungiyar WTO sun tattauna kan tasirin matakan kare yanayin ciniki a taron yini biyu na kwamitin kasuwanci da muhalli, wanda aka kammala jiya Laraba a birnin Geneva na kasar Switzerland.

Shawarar da kasar Sin ta gabatar ta yin shawarwari tsakanin bangarori daban-daban kan tsarin daidaita iyakokin carbon da kungiyar EU ta yi ta jawo hankalin kasashe mambobin kungiyar WTO. Hakan ya nuna cewa, manufofin kiyaye muhalli sun zama mataki na tabbatar da burin kiyaye muhalli. (Amina Xu)