logo

HAUSA

Xi Jinping: Za mu ci gaba da raya kasa mai karfi da farfado da al’ummar Sinawa

2023-03-13 10:29:04 CMG Hausa

 

Yau ne, aka rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC a dakin taron jama’a da ke birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin kana shugaban kwamitin tsakiyar rundunar sojan kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cikin jawabinsa a yayin bikin rufe taron cewa, za mu ci gaba da raya kasar Sin mai karfi gami da farfado da al’ummar Sinawa, kamar yadda kaka da kakaninmu suka yi a baya.

Xi ya bayyana cewa, al’ummar Sinawa sun cimma gagaruman nasarori a tarihi, tare da jure wahalhalu masu yawa. Bayan kafuwar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ta hanyar hada kan al’ummomim kabilu daban daban na kasar da kuma ba da jagora wajen yin gwagwarmaya har tsawon shekaru fiye da 100, don sake dawo mutuncinmu. Al’ummar Sinawa sun dawo da makomarsu a hannunsu. Al’ummomin Sinawa sun sake tsayawa da kafaffunsu, sun samu wadata. Yanzu suna kokarin raya kasarsu mai karfi. Ba wanda zai iya hana babban sha’anin farfado da al’ummar Sinawa. Kar a ci amanar jama’a. Wajibi ne a shugabanni su sauke nauyin da zamani da kuma tarihi ya dora musu, su ba da tasu gudummowa wajen kara azama kan raya kasar Sin mai karfi da farfado da al’ummar Sinawa, kamar yadda kaka da kakaninsu suka yi a baya. (Tasallah Yuan)