logo

HAUSA

Gamayyar kasa da kasa sun nuna maraba da yadda aka maido da huldar diplomasiyya a tsakanin Saudiyya da Iran

2023-03-13 14:14:16 CMG Hausa

Bisa goyon bayan kasar Sin, daga ranar 6 zuwa 10 ga wata, kasashen Saudiyya da Iran sun gudanar da shawarwari a birnin Beijing. A ranar 10 ga wata, kasashen biyu sun cimma yarjejeniya, kuma kasashen Sin da Saudiyya da Iran sun bayar da hadaddiyar sanarwa, inda suka sanar da maido da huldar diplomasiyya a tsakanin Saudiyya da Iran, tare da jaddada cewa, kasashen uku za su yi kokarin kiyaye ka’idojin kasa da kasa, da ma sa kaimin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya fitar da sanarwa cewa, kyakkyawar huldar dake tsakanin Saudiyya da Iran na da matukar muhimmanci wajen kiyaye kwanciyar hankali a yankin Gulf, don haka ya bayyana godiya ga kasar Sin bisa irin kokarin da kasar ta yi wajen ingiza yin shawarwari a tsakanin kasashen biyu.

Har wa yau, kungiyoyin duniya da kasashe da dama, ciki har da majalisar Larabawa da Palasdinu da kuma Lebanon sun bayar da sanarwa, inda suka yi maraba da yadda aka maido da huldar diplomasiyya a tsakanin Saudiyya da Iran, tare da yabawa irin rawar da kasar Sin ta taka. (Lubabatu)