logo

HAUSA

Rashin daidaiton samun alluran COVID-19 ya haifar da mutuwar da za a iya magancewa

2023-03-13 11:52:40 CMG Hausa

 

            

Wata budaddiyar wasika da aka rubura ta nuna cewa, da a ce an raba alluran rigakafin COVID-19 a duniya cikin adalci, da an ceci rayukan a kalla mutane miliyan 1.3 a cikin shekarar farko ta raba alluran, ko kuma da an kare mutuwar mutum daya a duk cikin dakika 24.

A cewar wasikar wadda gamayyar kungiyar samar da alluran ga jama’a wadda ke zama hadin gwiwar kungiyoyi da cibiyoyi sama da 100 don inganta hanyoyin da mutane ke samun alluran rigakafi ta rubuta, a yayin bikin cika shekaru 3, tun bayan da hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana barkewar COVID-19 a matsayin annobar da ke shafar daukacin duniya, "Mun kuma ga matakan da duniya ta dauka ta hanyar neman cin riba da kare muradun kasa fiye da batun rigakafin.

Wasikar ta kara da cewa, a maimakon a raba alluran rigakafin, da gudanar da gwaje-gwaje da jiyyar masu kamuwa da cutar ta hanyar la'akari da bukata, sai kamfanonin harhada magunguna suka kara yawan ribar da suke samu ta hanyar sayar da alluran da farko ga kasashe masu arziki. (Ibrahim)