logo

HAUSA

Wakilin Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Yi Watsi Da Ikirarin Fifita Wasu Al'adu Da Cin Karo Na Wayewar Kai

2023-03-11 16:35:09 CMG Hausa

Mukaddashin jakadan kasar Sin a MDD Dai Bing ya fada jiya Jumma'a cewa, tilas ne a yi kokarin yin fatali da da'awar da suka hada da fifita wasu al'ummomi da cin karo da wayewar kai.

Dai Bing, ya shaidawa babban taron bikin tunawa da ranar yaki da nuna kyamar musulunci ta duniya karo na farko, wanda ministan harkokin wajen kasar Pakistan Bilawal Bhutto Zardari da shugaban babban taron MDD Csaba Korosi suka shirya cikin hadin gwiwa, a hedkwatar MDD dake a birnin New York na kasar Amurka cewa, idan har ana son a yi yaki da nuna kyama da addinin Islama, da farko, wajibi ne mu tabbatar da daidaito. Kowane wayewar kai da addini yana da muhimmanci, kuma babu wanda ya fi wasu. Haka kuma tilas ne mu yi watsi da ikirarin nuna fifiko ga wasu wayewar kai da ma cin karo da wayewar kai.

Ya ce, wajibi ne mu taimakawa kasashe wajen zabar hanyoyin ci gaba da suka dace da yanayin kasashensu, da samar da ci gaba da zai shafi kowa, da nuna adawa da mayar da wasu saniyar ware, da sanya takunkumi na kashin kai.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a kawar da “guba” masu kyamar addinin musulunci a yayin taron da aka shirya game da ranar yaki da nuna kyama ga addinin musulunci ta duniya. Yana mai cewa, tilas ne mu fahimci bambanci, ba wai a matsayin barazana ba, amma a matsayin wadatar al'ummominmu. Wannan yana nufin bunkasa harkokin siyasa, da al'adu da tattalin arziki a cikin hadin gwiwar zamantakewa. (Ibrahim)