logo

HAUSA

An rufe taro kan kasashe mafiya karancin ci gaba na MDD karo na 5

2023-03-10 14:00:37 CMG Hausa

An rufe taro kan kasashe mafiya karancin ci gaba na MDD karo na biyar a Doha, babban birnin kasar Qatar a jiya Alhamis.

Yayin taron an zartad da Sanarwar Doha, inda aka yi alkawarin za a dauki manufofi a fannonin samar da isashen hatsi da ba mata ilmi da jari, da sauransu. Haka kuma, za a tabbatar da ganin an gudanar da “Ka’idodin Daukar Matakan Neman Ci Gaba Na Doha”, ta yadda za iya tabbatar da ganin kasashe 46 mafiya karancin ci gaba sun koma kan hanyar neman samun ci gaba mai dorewa cikin shekaru 10 masu zuwa.

Mataimakiyar babban sakataren MDD, Amina Mohammed, ta bayyana a yayin rufe taron cewa, kokarin sanya kasashe masu fama da koma baya, su samu ci gaba mai dorewa shi ne muhimmin abu dake cikin ajandar ci gaba mai dorewa na nan da shekarar 2030 ta MDD, don haka ya zama dole al’ummun kasa da kasa su tabbatar da ganin ba a bar kowace kasa a baya ba.

An bude taron kan kasashe mafiya karancin ci gaba na MDD karo na biyar ne a Doha, a ranar 5 ga wata. Kuma jigon taron shi ne “Mayar da damammaki zuwa ci gaba mai dorewa”. Ma’anar kasashe mafiya karancin ci gaba ita ce, kasashe wadanda suke cikin yanayi mafi koma baya a fannonin zamantakewa da tattalin arziki da kuma ci gaban bil’adam. Kawo yanzu, kasashe 46 ne MDD ta tabbatar da cewa su ne mafiya karancin ci gaba. (Safiyah Ma)