logo

HAUSA

Mazaunin HK ya yi bayani kan wadatar yankin a taron UNHRC

2023-03-09 15:42:32 CMG Hausa

Wani matashi na yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin mai kula da harkokin kungiyar MDD ta kasar Sin Huang Ziqian, ya gabatar da jawabi a yayin taro karo na 52 na hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD da aka kira jiya, inda ya yi bayani kan yadda aka farfado da wadata da kwanciyar hankali a yankin na Hong Kong.

Huang Ziqian ya bayyana cewa, tun bayan da aka aiwatar da dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong shekaru uku da suka gabata, an maido da kwanciyar hankali a yankin, kuma ana iya cewa, dokar tsaron kasa ta HK ta taka rawa matuka wajen tabbatar da tsaro da wadata da hakkin dan Adam a yankin.

Matashin ya yi tsokaci cewa, alkaluman kididdigar da bankin duniya ya fitar a shekarar 2021 sun nuna cewa, ma’aunin tafiyar da harkokin yankin Hong Kong bisa doka ya kai kaso 90 bisa dari, inda ya bukaci wadanda ke shafawa dokar tsaron kasa ta yankin Hong Kong bakin fenti da su daina tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, haka kuma su yi kokarin kyautata yanayin kare hakkin dan Adam da kasashensu ke ciki. (Jamila)