logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a gaggauta cika alkawarin tabbatar da tsaron mata

2023-03-08 13:11:08 CMG Hausa

Mataimakiyar darektan hukumar kula da harkokin mata da yara ta majalisar gudanarwar kasar Sin Lin Yi, ta yi kira ga zaman takewar al’ummar kasashen duniya da su kara zuba jari domin gaggauta cika alkawarin da aka yi kan aikin tabbatar da kwanciyar hankali da tsaro na mata.

Lin Yi ta yi tsokacin ne a muhawarar bainar jama’a da kwamitin sulhun MDD ya kira jiya Talata, inda ta yi bayani kan sakamakon da kasar Sin ta samu wajen tabbatar da daidaiton jinsi tsakanin mata da maza.

Madam Lin ta kara da cewa, an zartas da kuduri mai lamba 1325 a taron kwamitin sulhun MDD shekaru 23 da suka gabata, inda aka sake bayyana alakar dake tsakanin mata da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kasar Sin tana aiwatar da manufar tabbatar da daidaito tsakanin mata da maza, kuma tana daukar matakan da suka dace, domin baiwa mata hakki da ‘yancinsu.

Kuma matsayin matan kasar Sin ya dagu a bayyane yayin da ake ingiza kokarin zamanintarwa irin na kasar Sin, haka kuma matan kasar suna kara jin dadin rayuwa.

Kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri mai lamba 1325 ne a shekarar 2000, kudurin dake zama irinsa na farko da ke nuna tasirin tashin hankali ga mata da ‘yan mata, da rawar da suke takawa wajen magance aukuwar tashin hankali, da kiyaye zaman lafiya, da daidaita rikici, da kuma shimfida zaman lafiya. (Jamila)