logo

HAUSA

Da wuya Sin ta samu sabbin nasarori a shekarar 2022

2023-03-05 10:02:31 CMG Hausa

Da safiyar yau 5 ga wata ne aka fara gudanar da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin wato NPC a nan birnin Beijing.

Yayin da firaministan kasar Sin Li Keqiang yake ba da rahoton aikin gwamnatin kasar a gun taron, ya yi nuni da cewa, Sin ta samu bunkasuwar tattalin arziki mai inganci da zaman lafiya a zamantakewar al’ummar kasar a shekarar 2022 yadda ya kamata, yana mai cewa, da wuya Sin ta samu sabbin nasarori a shekarar 2022.

Li ya bayyana cewa, a shekarar bara, yawan GDPn kasar Sin ya karu da kashi 3 cikin dari, kuma karin wasu mutane miliyan 12 da dubu 60 sun samu aiki, kana farashin kayyayakin da jama’a suke kashe kudi kansu ya karu da kashi 2 cikin dari. Ya ce bisa sauyin yanayin mai sarkakiya da ake ciki, Sin ta cimma muhimmin burin samun bunkasuwar kasar na shekarar, yana mai cewa, Sin tana da karfin samun ci gaban tattalin arzikinta. (Zainab)