logo

HAUSA

Sin ta kasance mai kokarin shimfida zaman lafiya da ba da gudummawa ga ci gaban duniya, da bin odar kasa da kasa

2023-03-05 11:08:46 CMG Hausa

A cikin rahoton aiki da gwamnatin kasar Sin ta gabatar a yau 5 ga wata, an ce, kasar Sin za ta ci gaba da martaba manufofin diflomassiya na tabbatar da ‘yancin kai da tafiyar da harkokinta da kanta da kuma tabbatar da zaman lafiya. Haka kuma, za ta bi hanyar neman samun bunkasuwa cikin lumana, da sada zumunta da hadin kai da kasa da kasa bisa ka’idoji biyar na zama tare cikin lumana, gami da martaba manufar bude kofa ga waje don moriyar juna da samun nasara tare. A ko da yaushe, kasar Sin na iyakar kokarinta wajen shimfida zaman lafiyar duniya, da bayar da gudummawa ga ci gaban duniya, da ma bin odar kasa da kasa.

Rahoton ya kuma nuna cewa, kasar Sin na son hada gwiwa da kasa da kasa wajen aiwatar da shawarar ci gaban duniya, da ta tsaron duniya, da yada ra’ayin bai daya na darajar bil Adama, a kokarin kara azama ga raya makomar bil Adama ta bai daya, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya.(Kande Gao)