logo

HAUSA

An kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar CPPCC

2023-03-04 16:15:58 CMG Hausa

An kaddamar da zaman farko na kwamitin majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin (CPPCC) karo na 14, da maraicen yau Asabar 4 ga wata a Beijing, fadar mulkin kasar.

Wannan ne taron shekara-shekara na farko da aka kira a cikin tsawon wa’adin aikin shekaru biyar na sabon kwamitin majalisar. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran wasu shugabannin kasar sun halarci bikin kaddamar da taron.

Wang Yang, shugaban kwamitin majalisar CPPCC karo na 13 ya gabatar da rahoton aiki na kwamitin a wajen taron.

Rahotanni na cewa, kwamitin majalisar CPPCC na 14 ya kunshi membobi 2169, daga wasu bangarori 34, ciki har da membobin da ba na jam’iyyar kwaminis ta kasar ba da yawan su ya kai kaso 60.8 bisa dari. A cikin taron tsawon kwanaki 7 da rabi, za su zabi sabbin shugabannin majalisar a sabon zagaye, ciki har da shugaba da mataimakin shugaba na majalisar, tare kuma da gudanar da shawarwari da tattaunawa kan wasu muhimman kudurori, wadanda suka shafi fannonin siyasa da tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma na kasar ta Sin.

Majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wato CPPCC a takaice, muhimmiyar hukuma ce ta hadin-gwiwar jam’iyyu daban-daban, gami da yin shawarwarin siyasa, karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar, kana wani muhimmin sashi ne na tsarin gudanar da harkokin kasa, wanda ke bayyana salon musamman na kasar. Ta hanyar yin shawarwarin siyasa, da sa ido bisa tafarkin demokuradiyya, da halarta gami da yin shawarwarin siyasa, majalisar CPPCC tana taka rawa ta musamman a fannin tsara manyan manufofin kasa da na kananan hukumomi, da sauran wasu fannonin da suka shafi siyasa, da tattalin arziki, da al’adu, da zaman rayuwar al’umma. (Murtala Zhang)