logo

HAUSA

Rukunin ciniki na Afirka na tattauna yiwuwar samar da tsarin sadarwa na bai daya a nahiyar

2023-03-03 13:50:52 CMG Hausa

Kungiyar hada-hadar ciniki ta Afirka ta fara wani taro na yini biyu jiya Alhamis a Nairobi na kasar Kenya, don tattauna yiwuwar samar da wani tsarin sadarwa na wayoyin salula na bai daya a nahiyar Afirka,

Taron ya hada kungiyoyin Gabashi da Kudancin Afirka COMESA, da kungiyar kasashen gabashin Afirka EAC da kungiyar raya kasashe ta IGAD da hukumar kula da tekun Indiya IOC da kungiyar raya kasashen kudancin Afirka SADC, da nufin duba hanyoyin rage farashin kiran waya a ciki da kuma sassan kungiyoyin raya tattalin arzikin kasashen.

A cewar Jean-Baptiste Mutabazi, jami’i mai kula da samar da kayayyakin more rayuwa da dabaru, na kungiyar COMESA, ya ce har yanzu farashin kiran waya na da tsada sosai a duk fadin nahiyar da ma tsakanin al'ummomin yankin nahiyar.

A nata bangare, Rosemary Mapolao Mokoena, darekta mai kula da kayayyakin more rayuwa ta kungiyar raya kudancin Afirka (SADC), ta ce kudaden kira daga wajen wata kasa, na kawo cikas ga hanyoyin sadarwa tsakanin kasashe daban daban, yayin da tsarin sadarwa na nahiyar Afirka na bai daya, zai amfani jama’ar kasashen Afirka. (Bello Wang)