logo

HAUSA

Kamfanin Ericsson: kamfanonin sadarwa na kasar Sin sun gaggauta rungumar fasahar 5G

2023-03-02 11:38:22 CMG Hausa

Magnus Ewerbring, babban jami’in kula da fasahohi na kamfanin sadarwa na Ericsson a yankin Asiya da Pasifik, ya ce kamfanonin sadarwa na kasar Sin sun yi gaggawar rungumar fasahar sadarwa ta 5G, kuma tuni suka fara cin moriyarta.

Magnus Ewerbring, ya bayyana yayin taron kamfanonin sadarwa na duniya ranar Talata, a birnin Barcelona na kasar Spaniya cewa, kamfanonin sadarwa na kasar Sin sun gaggauta rungumar fasahar sadarwa ta 5G, inda suka fara amfani da ita tare da samar da moriya ga al’ummominsu. Yana mai cewa kasar Sin ta gina tsarukan sadarwa na 5G kuma fasahar ta mamaye yankuna da dama.

Ya ce shekaru 5 ke nan, komai na tafiya yadda ya kamata a kasar Sin. Kuma dukkan kamfanonin sadarwa 3 na kasar, sun samu ci gaba sosai kuma suna samar da hidimomin 5G. Ya nanata cewa suna farin cikin goyon bayan wannan al’amari.

Ya kara da cewa, akwai dimbin damarmaki dake tattare da samar da tsarin sadarwa ga mutane da harkokin kasuwanci, domin samun damar gudanar da abubuwa yadda ya kamata, kuma nahiyar Asiya da ma kasar Sin sun kasance kyakkyawan misali. (Fa’iza Mustapha)