logo

HAUSA

Shugabar yawon bude ido ta Australia tana kan hanyar kawo ziyara kasar Sin

2023-03-01 11:30:22 CMG Hausa

Hukumar yawon bude ido ta kasar Australia (TA) ta kaddamar da wani gangami na bunkasa kasuwar yawon bude ido ta daya a duniya, wato kasar Sin.

Yau ne shugabar gudanarwar hukumar Phillipa Harrison, ta tashi zuwa kasar Sin, don gudanar da ziyarar kwanaki uku a biranen Guangzhou, da Beijing da kuma birnin Shanghai, inda za ta gana da abokan hulda bisa manyan tsare-tsare, a wani yunkuri na gayyatar masu yawon bude ido na kasar Sin zuwa Australia.

A cewar kamfain dillancin labarai na Australia, kafin barkewar annobar COVID-19, Sinawa dake ziyartar kasar, sun kai kusan kashi 15 cikin 100, na dukkan masu yawon bude ido na kasashen waje dake zuwa Australia, da kashi 1 bisa 3 na kudaden da masu yawon bude ido ke kashewa a kasar.

Ana sa ran ya zuwa karshen shekarar 2023, karfin zirga-zirgar jiragen sama tsakanin kasashen, zai kai kashi 80 cikin 100, na matakan da aka dauka gabanin annobar COVID.

Ta bayyana cewa, tana fatan ganawa da manyan abokan huldar kamfanonin jiragen sama na kasar Sin, game da damammakin kara yawan zirga-zirgar jiragen sama zuwa Australia.

Ta ce, karfin yanayin zirga-zirgar jiragen sama, shi ne mabudin ci gaban kasuwannin kasar Sin. Tana mai cewa, wadannan taruka za su kasance masu muhimmanci yayin da kasarta ke kara kaimi wajen kaddamar da babban gangami a kasar Sin a tsakiyar wannan shekara. (Ibrahim Yaya)