logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika sakon jaje ga takwararsa ta kasar Girka Katerina Sakellaropoulou

2023-03-01 20:42:30 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aika sakon jaje ga takwararsa ta kasar Girka, Katerina Sakellaropoulou, game da hadarin jiragen kasa da ya auku a kasar, yau Laraba.

Xi Jinping ya bayyana cewa, ya na cike da alhinin hadarin jiragen kasa da ya faru, wanda ya haddasa mutuwar mutane da kuma raunatar wasu masu dimbin yawa. Ya ce a madadin gwamnatin kasar Sin da kuma jama’ar kasar, yana jaje tare da mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu, tare da yi wa wadanda suka ji raunuka fatan samun sauki cikin sauri.(Safiyah Ma)