logo

HAUSA

Belen Fernandez: Martanin da Amurka ta mayar kan balan-balan na yanayi na kasar Sin babban aikin soja ne

2023-02-28 09:51:36 CMG HAUSA

 

Wani ra'ayi da aka wallafa a shafin yanar gizo na Al Jazeera ya bayyana cewa, martanin da Amurka ta mayar kan balan-balan din yanayi na kasar Sin da ya kauce hanyarsa, ya yi watsi da tarihinta na "sanya ido da kan harin bama-bamai a duniya."

Sharhin mawallafiyar mai suna Belen Fernandez da aka wallafa ranar Alhamis din da ta gabata, ya bayyana harbo balan-balan din da Amurka ta yi a sararin samaniyarta, wani abu ne da aka yi da gangan, wanda ya baiwa duniya mamaki

Matakin da Amurka ta dauka rashin fahimta ne, idan aka yi la'akari da nata tarihin sanya ido kan kowa da ma komai a cikin duniya, ciki har da gomman shekaru da ta shafe tana leken asiri na musamman kan kasar Sin.

A cewar Fernandez, Amurka na fuskantar tarin matsaloli wadanda ke da matukar hadari fiye da balan-balan da iska ta kada shi gabar tekun South Carolina, kamar rashin ingantaccen tsarin kiwon lafiya ko tsarin ilimi da harbin jama'a.

Ta kara da cewa, firgicin da ake yi game da balan-balan na kasar Sin ya nuna cewa, bai kai ta'addancin da ake yi a Amurka ba, kama daga harin bama-bamai da kai hare-hare a kasashen Afganistan da Iraki har zuwa gurbata sararin samaniya da jiragen sama marasa matuka. (Ibrahim Yaya)