logo

HAUSA

Shugabar kwamitin EU ta yi kira da yin kwaskwarima kan ka’idojin ba da kariya ga ‘yan gudun hijira

2023-02-27 14:08:39 CMG Hausa

Shugabar hukumar tarayyar Turai EU Ursula von der Leyen ta yi kira ga yin kwaskwarima kan ka’idojin ba da kariya ga ‘yan gudun hijira bayan mutuwar ‘yan gudun hijira fiye da 50 a wajen kasar Italiya.

Rahotanni sun bayyana cewa, da sanyin safiyar jiya Lahadi, wani jirgin ruwa dake dauke da ‘yan gudun hijira ya gamu da hadari a gabar kudancin kasar Italiya, wanda ya haddasa mutuwar mutane a kalla 59, cikin har da kananan yara 12. (Zainab)