logo

HAUSA

Dubban mutane ne suka yi zanga-zanga a Berlin domin adawa da ba Ukraine makamai

2023-02-26 17:44:44 CMG Hausa

Mutane sama da 10,000 ne suka yi zanga-zanga a kasar Jamus, inda suke kira da a daina turawa Ukraine manyan makamai, tare da kira ga shugaban gwmnatin kasar, Olaf Scholz da ya jagoranci wani yunkurin diflomasiyya da zai kawo karshen bude wuta da samar da yarjejeniyar zaman lafiya

Zanga-zangar ya zo ne kwana guda bayan cika shekara 1 da fara rikici tsakanin Rasha da Ukraine, inda kasashen yamma suka yi alkawarin samar da karin makamai ga Ukraine, da kakaba sabbin takunkumai kan Rasha da zummar bayyana goyon baya ga Ukraine.

Mashirya zanga-zangar sun bayyana a shafin yanar gizo cewa, suna son shugaban gwamnatin Jamus ya dakatar da tsanantar tura makamai. Saboda a kullum akan yi asarar adadin rayukan da ya kai 1,000, lamarin da gab yake da rikidewa zuwa yakin duniya na 3.

Jamus tare da Amurka, sun kasance manyan masu samar da makamai ga Ukraine. A cewar Olaf Sholz a ranar Alhamis, tallafin Jamus ga Ukraine da ya kunshi na kudi da kayayyakin jin kai da makamai, ya kai sama da euro biliyan 14, kwatankwacin dala biliyan 14.83. kuma bisa rahoton cibiyar Statista, zuwa ranar 15 ga watan Junairu, tuni tallafin Amurka ga Ukraine ta fuskar kudi domin ayyukan soji , ya tsamma dala biliyan 46.6. (Fa’iza Mustapha)