logo

HAUSA

An kammala taron ministocin kudi na kasashen G20 a India

2023-02-26 17:46:08 CMG Hausa

Ministocin kudi da gwamnonin manyan bankunan kasashen kungiyar G20, sun kammala taronsu yau Asabar a kasar India, inda suka jaddada kudurinsu na inganta manufar hadin kan duniya da jagorantar tattalin arzikin duniya wajen samun karfi da ci gaba na bai daya.

Sun kuma bayyana bukatar dake akwai ta magance matsalar basussuka a kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga.

Yayin kammala taron na yini biyu a birnin Bengaluru na kudancin India, an fitar da daftarin dake kunshe da sakamakon taron, wanda ya bayyana cewa, an samu ingantuwar kan hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya da aka yi yayin taronsu na watan Oktoban 2022.

Sai dai, a cewar daftarin, ci gaban tattalin arzikin na tafiyar hawainiya, kuma kalubalen da aka yi hasashe na karuwa, ciki har da hauhawar farashin kayayyaki da sake barkewar annoba da tsaurara sharuddan da suka shafi hada-hadar kudi wadanda ka iya tsananta matsalar biyan bashi ga kasashe masu tasowa.

Har ila yau, a karshen tattaunawar ta jiya Juma’a, kasashen G7 da suka hada da Canada da Faransa da Jamus da Italiya da Japan da Birtaniya da Amurka, sun sanar da kakaba sabbin takunkumai kan Rasha, saboda matakinta kan Ukraine. (Fa’iza Mustapha)