logo

HAUSA

UN: Takardar matsayar kasar Sin game da rikicin Ukraine muhimmiyar gudummawa ce

2023-02-25 16:24:04 CMG Hausa

Stephane Dujarric, mai magana da yawun babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, takardar matsayar kasar Sin game da warware rikicin Ukraine a siyasance, wata muhimmiyar gudummawa ce. Yana mai cewa, kiran da aka yi na kaucewa amfani da makaman nukiliya yana da matukar muhimmanci.

A jiya Juma'a ne, kasar Sin ta fitar da wata sanarwa, inda a cikinta ta bayyana matsayinta kan batun sasanta rikicin kasar ta Ukraine a siyasance, tana mai cewa tattaunawa ita ce kadai mafita mafi dacewa wajen warware rikicin na Ukraine.(Ibrahim)