logo

HAUSA

Wang Yi ya yi bayani kan ziyararsa a kasashen Turai da Rasha

2023-02-24 10:40:56 CMG Hausa

A ranar 22 ga wata, Wang Yi, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana darektan ofishin hukumar kula da harkokin waje ta kwamitin kolin ya bayyana cewa, yadda kokarin kasar Sin na zamanintar da kanta zai amfani kasar da ma duniya baki daya. Sin ta riga ta cimma gagarumar nasara wajen dakile da kandagarkin cutar COVID-19, ana farfado da tattalin arziki da zamantakewar al’ummarta, lamarin da ya sa kasar Sin za ta ci gaba da zama muhimmin injin na sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Bisa dimbin hakikanan abubuwa, kasar Sin ta shaida cewa, neman ci gaba cikin lumana ba kawai wata hanya ce mai yiyuwa ba,amma wata hanya ce mai dacewa sosai. Sin za ta ci gaba da bin hanyar, tare da fatan yin kokari tare da sauran kasahe wajen bin hanyar neman ci gaba cikin lumana.

Wang Yi ya yi wannan furuci ne a gaban wakilan kafofin watsa labarai, bayan da ya kammala ziyararsa a kasashen Faransa, Italiya, Hungary da Rasha, da kuma halartar taron tsaro na Munich karo na 59.

Kasar Amurka tana ta kara gishiri kan batun balan-balan maras matuki na kasar Sin da ya shiga sararin saman Amurka bisa kuskure, don haka kasashen duniya sun mai da hankali sosai kan kwarya-kwaryar ganawa a tsakanin bangarorin biyu a yayin taron tsaron Munich. Game da batun, Wang Yi ya nuna cewa, yayin da yake ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya kalubalanci Amurka da ta dakatar da yin wannan abun wauta don biyan bukatunta a siyasance. Ya kamata Amurka ta yi kokari da sahihiyar zuciya wajen warware matsalar da za ta kai ga lalata dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu sakamakon wannan batu. Amma idan Amurka na son kara tsananta wannan batu, tabbas kasar Sin za ta ci gaba da mayar da martani har zuwa karshe. (Kande Gao)