logo

HAUSA

Wakilin Sin a MDD ya yi kira ga kasashen Rasha da Ukraine da su tsagaita bude wuta

2023-02-24 19:38:16 CMG Hausa

A yau ne, kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da taron bainar jama’a kan hadin gwiwa da kungiyar Tarayyar Turai (EU). A jawabin da ya gabatar a yayin taron, jakadan Sin dake MDD, Dai Bing, ya yi kira ga kasashen Rasha da Ukraine da su gaggauta tsagaita bude wuta, da cimma daidaiton tsaro a nahiyar Turai ta hanyar tuntubar juna, da tattaunawa.

Bangaren kasar Sin ya bayyana cewa, rikicin kasar Ukraine babban kalubale ne ga tsaron kasashen Turai. Don haka Sin tana kira ga kasashen Rasha da Ukraine da su gaggauta tsagaita bude wuta, kana EU, da NATO, da Amurka su ma su shiga tuntuba da tattaunawa da kasar Rasha, domin cimma daidaiton tsaro a nahiyar ta Turai.

Dai Bing ya kara da cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan samar da zaman lafiya da tattaunawa nan da nan, da son ci gaba da taka rawar da ta dace wajen warware rikicin kasar Ukraine. (Ibrahim)