logo

HAUSA

An ba da rahoto kan gaskiyar gibin dake tsakanin matalauta da masu arziki mai tsanani na Amurka

2023-02-23 20:11:50 CMG HAUSA

 

Yau 23 ga wata, an ba da rahoton gaskiya game da mummunan gibin dake tsakanin matalauta da masu arziki a Amurka, inda aka gabatar da hakikanin hali da ake ciki da wasu alkaluma, don fayyace halin da ake ciki a Amurka, wato gibin dake tsakanin matalauta da masu arziki ya kara tsananta, da kuma dalilan siyasa da suka haifarwa al’umma da wannan matsala da ba za a iya warware ba.

Rahoton na nuna cewa, Amurka ita ce kasa mafi karfi a bangaren tattalin arziki, kuma kasa da ta fi fama da gibin kudaden shiga, inda matalauta suka kara talaucewa yayin da masu arziki suka kara arziki. Tun lokacin barkewar COVID-19, kasar ta dauki dimbin matakan ingiza bunkasuwar tattalin arziki da hada-hadar kudi, amma ba su taimakawa matalauta daga tushe ba, matakin da baiwa masu arziki damar samun karin kudade, inda gibin dake tsakaninsu ya kara karuwa.

Ban da wannan kuma, rahoton ya nuna cewa, wannan ginbi ya zama wata matsala da ta dade tana kasancewa a cikin al’ummar Amurka, ya kamata gwamnatin Amurka ta duba halin da ake ciki, ta saurarin bukatun jama’a, ta yadda za a magance wannan matsala. (Amina Xu)