logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga al’ummar kasa da kasa da ta kara mai da hankali kan batun Somaliya

2023-02-23 13:43:57 CMG Hausa

Jiya ne mataimakin zaunennen wakilin kasar Sin a MDD, Dai Bing, ya gabatar da jawabi a yayin taron kwamitin sulhu na MDD kan batun Somaliya, inda ya yi kira ga al'ummomin kasa da kasa, da su ci gaba da kara mai da hankali da zuba jari a cikin kasar Somaliya.

Dai Bing ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, an samu sauyi a fannin ayyukan yaki da ta'addanci a kasar Somaliya, amma har yanzu lamarin yana da sarkakiya da tsanani, yanayin tsaro bai inganta sosai ba, kuma akwai damuwa a fannin matsalar jin kai. Don haka, ya kamata kasashen duniya su ci gaba da kara mai da hankali kan lamarin kasar Somaliya. Ya kamata gwamnatin Somaliya ta kara yin kokarin ganin an dade mata takunkumin da aka kafa kan ayyukan jin kai, da inganta ayyukan jin kai, da ba da tabbaci mai karfi don biyan bukatun tsaro da ci gaban al'ummar kasar Somaliya.

Dai Bing ya ce a baya-bayan nan, rahoton MDD ya nuna cewa, ayyukan yaki da ta'addanci a Somaliya na iya yin mummunan tasiri kan yanayin jin kai, musamman batutuwan da suka hada da tilastawa matasa shiga aikin soja. Kasar Sin ta yi kira ga ayyukan soji da abin ya shafa, da su mai da hankali wajen kare fararen hula, musamman ma masu rauni kamar mata da kananan yara, da kokarin kawar da mummunar illar da hakan zai iya haifarwa. (Safiyah Ma)