logo

HAUSA

An Yi Ganawa Tsakanin Jami’an Sin Da Rasha Ta Fuskar Manyan Tsare-tsare Da Tsaro

2023-02-22 10:06:41 CMG Hausa

Wang Yi, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana darektan ofishin hukumar kula da harkokin waje ta kwamitin tsakiyar jam’iyyar, da Nikolai Patrushev, sakataren taron tsaron kasar Rasha sun gana da juna jiya Talata a birnin Moscow, hedkwatar kasar Rasha, a matsayin jami’an kula da tsarin tattaunawa tsakanin kasashen Sin da Rasha dangane da manyan tsare-tsare da tsaro.

A yayin ganawar, sassan biyu sun nuna fatansu na ci gaba da martaba manufar cudanyar sassa daban daban, nuna adawa da danniya ta ko wane irin salo, da kara azama kan bunkasa hulda a tsakanin kasa da kasa bisa ka’idar demokuradiyya da raya duniya a matakai daban daban. Har ila yau sassan 2, sun amince da ci gaba da inganta hadin gwiwarsu karkashin tsarin cudanyar sassa daban daban, da kara kokarin kyautata tafiyar da harkokin duniya yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)