logo

HAUSA

Sin na nacewa kan hanyar raya hakkin dan Adam irin nata

2023-02-19 16:01:27 CMG Hausa

Kwanan baya tawagar wakilan kasar Sin ta halarci taron bincike karo na uku kan yadda ake aiwatar da “yarjejeniyar kasa da kasa game da kare ‘yancin tattalin arziki da zaman takewar al’umma da al’adu” da aka shirya a birnin Geneva na kasar Switzerland. Bayan taron, zaunannen wakilin kasar dake Geneva Chen Xu ya zanta da wakilin CMG, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan hanyar raya hakkin dan Adam irin nata, kuma ta ba da babbar gudummowa kan ingiza da kare ‘yancin tattalin arziki da zaman takewar al’umma da al’adu a fadin duniya.

Chen Xu ya kara da cewa, har kullum gwamnatin kasar Sin tana martaba ka’idojin MDD da ruhin “sanarwar hakkin dan Adam na duniya”, tana kuma mutunta dokar kasa da kasa game da kare hakkin dan Adam, kuma ta hada ka’idar kare hakkin dan Adam da hakikanin yanayin da kasar take ciki, domin ciyar da tattalin arziki da zaman takewar al’ummarta gaba yadda ya kamata.

Haka zalika, Chen Xu ya bayyana cewa, burin farfado da al’ummar kasar Sin, shi ne tabbatar da adalci tare kuma da ingiza ci gaban aikin kare hakkin dan Adam. Kasar Sin tana maraba ga bangarori daban daban da su binciki sakamakon da kasar Sin ta samu wajen aiwatar da yarjejeniyar, kuma za ta amince da hakikanin sharhin da za a yi mata da zuciya daya. (Jamila)