logo

HAUSA

Wang Yi: Ya kamata Sin da EU su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu

2023-02-19 16:06:14 CMG Hausa

Babban jami'in diflomasiyyar kasar Sin Wang Yi, ya bayyana a jiya Asabar cewa, yayin da duniya ke fuskantar sauye-sauye da rudani, ya kamata kasashen Sin da Turai su karfafa hadin gwiwa don kara samun kwanciyar hankali a duk duniya.

Wang, dake zama darektan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS, ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da babban wakilin kungiyar EU mai kula da harkokin waje da manufofin tsaro Josep Borrell a yayin taron tsaro na Munich karo na 59.

Wang, wanda har ila mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya bayyana cewa, Sin da EU abokan hadin gwiwa ne, ba abokan hamayya ba ne, kuma ra'ayinsu ya zarce sabanin da ke tsakaninsu.

A nasa jawabin Borrell ya bayyana cewa, a ko da yaushe bangaren Turai yana inganta dangantakar EU da Sin bisa gaskiya da sanin ya kamata, yana mai jaddada cewa, kungiyar EU na tsayawa tsayin daka, kan manufar Sin daya tak a duniya, ta kuma amince da gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin a matsayin halattacciyar gwamnatin da ke wakiltar daukacin jama’ar kasar Sin. Kana yana goyon bayan kokarin da kasar Sin ke yi na kare ikon mallakar kasa da cikakken yankunanta, kuma za ta aiwatar da ka'idar zuwa hadin gwiwar siyasa tsakanin kungiyar ta EU da kuma kasar Sin.(Ibrahim)