logo

HAUSA

Wang Yi: Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta aikata

2023-02-19 15:46:42 CMG Hausa

A jiya Asabar ranar 18 ga wannan wata, agogon kasar Jamus, mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS kuma darektan ofishin hukumar harkokin waje ta kwamitin kolin Wang Yi ya halarci taron tsaro a birnin Munich na kasar Jamus, inda ya gabatar da muhimmin jawabi, tare kuma da amsa tambayoyin da aka yi masa.

Wang Yi ya yi tsokaci cewa, yanzu ana mai da hankali matuka kan batun balan balan maras matuki na kasar Sin da ya shiga samaniyar kasar Amurka bisa kuskure, inda Amurka ta siyasantar da batun. Kasar Sin ta riga ta gayawa Amurka cewa, balan balan din ba na aikin soji ba ne, ya kauce hanyar da yake bi, ya shiga samaniyar Amurka sakamakon kadawar iska, don haka kasar Sin ta bukaci Amurka da ta kai zuciya nesa ta daidaita batun tare da kasar Sin.

Amma abun bakin ciki shi ne, Amurka ta yi biris da hakikanin abubuwan da suka faru, ta tura jirgin saman yaki, ta harbo balan balan din da bai haifar da kalubale, matakin da Amurka ta dauka ya sabawa yarjejejiyar kasa da kasa da abin ya shafa. Kuma kasar Sin ba ta amince da hakan ba, ta riga ta soki lamarin da ma nuna adawa ga Amurka.

Game da rikicin kasar Ukraine, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta damu kan rikicin, tana fatan bangarorin da abin ya shafa, za su yi shawarwari domin daidaita batun yadda ya kamata, saboda burin kasar Sin shi ne tabbatar da tsaro a duniyarmu.

Yayin taron tsaron na Munich, Wang Yi ya yi kwarya kwaryar ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, inda ya bayyana matsayin kasar Sin kan batun balan balan din. (Jamila)