logo

HAUSA

Wakilin Sin Ya Bukaci NATO Da Ta Ba Da Gudummawar Da Ta Dace Ga Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali A Duniya

2023-02-18 16:20:09 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun ya bayyana cewa, ya kamata kungiyar tsaro ta NATO, ta ba da gudummawa mai kyau ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, maimakon kasancewa mai tayar da hankali kawai.

Zhang ya shaidawa taron kwamitin tsaro game da batun Ukraine jiya Jumma’a cewa, “muna kira ga NATO da ta koyi darasi daga tarihi, ta yi watsi da tunanin yakin cacar baka, da neman yin fito-na-fito da adawa da juna, da kuma dakatar da ayyuka masu hadari na haifar da makiya, da hargitsa yankin Turai, da ma kawo illa ga yankin Asiya da tekun Fasifik.”

Jakada Zhang ya kuma bayyana cewa, a hannu guda kungiyar NATO tana ikirarin ci gaba da zama kawancen tsaro na yankin, yayin da a daya bangaren kuma take kokarin keta iyakokinta na kasa da fadada manufofinta, da haifar da rarrabuwar kawuna, da tada zaune tsaye, da haifar da fargaba da fada da juna, da ci gaba da karfafa alakar soja da tsaro da kasashen Asiya da tekun Fasifik, wannan a fili ya saba wa abin da take fada.

Wakilin ya kuma jaddada cewa, rikicin Ukraine, tashe-tashen hankula ne da ake fama da su a Turai, wanda ke da alaka ta kut-da-kut da yadda kungiyar tsaro ta NATO ke neman fadada tasirinta a gabashin kasar tun bayan yakin cacar baka.

Ya kara da cewa, kokarin neman cikakken tsaro da kebewar siyasa da amfani da karfi a kan wani bangare, shi ne ainihin dalilin da ya sa Turai ke cikin matsalar tsaro, idan aka bi irin wannan tunani, to kuwa Turai, da ma duniya baki daya za su shiga cikin rudani mafi girma. (Ibrahim)