logo

HAUSA

Kayayyakin jin kai da gwamnatin Sin ta baiwa Syria sun isa birnin Damascus

2023-02-16 15:48:21 CMG Hausa

A jiya Laraba ne kayayyakin jin kai na yaki da bala’in girgizar kasa, da gwamnatin Sin ta baiwa kasar Syria, suka isa birnin Damascus, fadar mulkin kasar ta Syria. Jakadan Sin dake Syria Shi Hongwei, da mataimakin ministan kula da jihohi, da hukumar muhallin hallitu Moataz Dawji, da sauran jami’ai, sun halarci filin jigin saman birnin don maraba da zuwan kayayyakin, da kuma halartar bikin mika su.

A jawabinsa yayin bikin, Shi Hongwei ya bayyana cewa, ko da yake Sin da Syria suna da nisa da juna, amma sun dade da kasancewa abokan arziki dake taimakawa juna, da kulawa da juna. Kuma kayayyakin jin kai da gwamnatin Sin ta bayar a wannan karo, sun hada da jakukkunan ba da agajin gaggawa, da rigunan sanyi, da tantuna da barguna.

Ban da wadannnan, akwai na’urorin taimakawa numfashi, da na’urorin sanya barci, da na’urorin sarrafa iskar oxygen, da sauran kayayyakin kiwon lafiya na gaggawa da ake bukata, wajen sake gina tsarin kiwon lafiya bayan bala’in.

Bugu da kari, ana fatan wadannan kayayyaki za su taimaki bangaren Syria, wajen kawar da mummunan tasirin da bala’in ya haifar, da farfado da yankunan da bala’in ya shafa.

Moataz ya ce, bisa goyon bayan da Sin da sauran kasashe abokantaka suka nuna, bangaren Syria yana da kwarin gwiwar shawo kan wahalhalun da bala’in ya haddasa, kuma zai sake gina kasar cikin sauri. (Safiyah Ma)