logo

HAUSA

Babban hafssan sojojin Nijar ya kai ziyara bayan mutuwar sojojin rukunin Almahaou A Intagarmey

2023-02-15 09:12:45 CMG Hausa

Daga ranar 12 zuwa 13 ga watan da muke ciki, babban hafsan sojojin jamhuriyar Nijar, janar Salifou Mody ya kai wani rangadin ba zata a sansanin soja na PMR dake Tiloa, bayan wani fito na fito tsakanin sojojin Nijar da dakarun kungiyoyin ’yan ta’adda a ranar Juma’a 10 ga watan Febrairun shekarar 2023 a yankin Intagarmey mai iyaka da kasar Mali.

Daga jamhuriyar Nijar, wakilinmu Mamane Ada ya aiko mana da rahoto. 

Bayan wani fito na fito tsakanin sojojin Nijar da dakarun kungiyoyin ’yan ta’adda a ranar Juma’a 10 ga watan Febrairun shekarar 2023 a yankin Intagarmey mai iyaka da kasar Mali, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar jojojin kasar Nijar guda 10, da bacewar wasu 16 da jikkita da dama, babban hafsan sojojin kasar Nijar, janar Salifou Mody ya kai wani rangadin ba zata daga ranar 12 zuwa 13 ga watan da muke ciki a sansanin soja na PMR dake Tiloa, shugaban sojojin ya samu rakiyar birgadiye-janar Mohamed Toumba dake kula da rakunin sojojin Almahaou da kuma rakiyar wasu manyan jami’an sojoji. Makasudin wannan rangadi na kwanaki biyu a wannan yanki shi ne na bada kwarin gwiwa ga rundunonin sojojin kasar da ke fagen daga, da kuma kimanta yanayin tsaro da kuma aiwatar da sabbin dubarun yaki. A lokacin ziyarar, babban hafsan sojoji  ya gana da daukacin sojojin da ke wurin da suka bayyana nacewa da juriya domin tabbatar da tsaron al’umomi da dukiyoyinsu. Haka kuma, janar Salifou Mody ya isar da sakon ta’aziya da goyon bayan hukumomin kasa daga farko shugaban kasar Nijar, Bazoum Mohamed. Daga karshe, tawagar ta ziyarci makabartar PMR dake Tiloa inda aka yi jana’izar sojojin da suka mutu.

Mamane Ada, daga Yamai zuwa sashen hausa na CRI.