logo

HAUSA

Shugaban Masar: Yanayin Palestinu zai kawo illa ga tsaron yankin

2023-02-13 13:53:11 CMG Hausa

Jiya Lahadi ne shugaban kasar Masar Abdel Fattah al Sisi, ya bayyana cewa, yanayi mai tsanani da Palestinu ke ciki, zai haifar da illa ga tsaron yankin, tare kuma da kawo cikas ga “shirin kafa kasashe biyu”.

Shugaba Sisi, da shugaban Palesdinu Mahmoud Abbas, da sarkin Jordan Abdullah Bin Al-Hussein II, da babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit, da wasu tawagogin manyan jami’ai na kasashen Larabawa, sun kira taro a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar, hedkwatar kungiyar kasashen Larabawan, domin tattaunawa game da tsanantar yanayi da yankin Palestinu da Isra’ila ke ciki a halin yanzu.

Yayin taron, shugaba Sisi ya yi tsokaci da cewa, bai kamata bangarori daban daban su dauki matakin sauya yanayin da birnin Kudus ke ciki a halin yanzu ba, saboda mai yiwuwa hakan ya yi mummunan tasiri ga tattaunawa tsakanin Palestinu da Isra’ila.

A nasa bangaren, Mahmoud Abbas ya bayyana cewa, Palestinu tana fatan MDD za ta tsai da kudurin bai wa Palesdinu damar kasancewa mambar majalisar a hukumance, domin tabbatar da “shirin kafa kasashe biyu”.

A cikin ‘yan makonnin da suka gabata, yanayin da yankin Palestinu da Isra’ila ke ciki yana kara tsanani, inda wasu mutane suka rasa rayuka sakamakon fito na fito da ya auku, tsakanin sojojin Isra’ila da Palestinawa, a yankin dake yammacin gabar kogin Jordan, da wasu unguwannin birnin Kudus.

A sakamakon hakan, Palestinu ta sanar da cewa, ta dakatar da hadin gwiwa da Isra’ila a bangaren tsaro, yayin da ita ma Isra’ilan ta sanar da matakan ramuwa da za ta dauka kan Palestinawa. (Jamila)