logo

HAUSA

Kayayyakin tallafin da Sin ta samarwa Turkiye a karon farko sun isa filin jirgin saman Istanbul

2023-02-13 13:49:52 CMG Hausa

A jiya Lahadi, jirgin saman dakon kayayyakin tallafin da gwamnatin kasar Sin ta samarwa kasar Turkiye, sakamakon aukuwar girgizar kasa mai tsanani a kasar sun isa filin tashi da saukar jiragen sama na Istanbul dake Turkiye, an kuma sauke dukannin kayayyakin tallafin a kasar.

Kayayyakin tallafin sun hada tantuna, da barguna, da sauran kayayyakin da yankunan da girgizar kasa ta shafa ke matukar bukata. Game da hakan, hukumomin da abun ya shafa a Turkiye sun bayyana cewa, za su raba kayayyakin bisa hakikanin bukatun wurare daban daban.

Haka zalika, an aike da kayayyakin tallafin jin kai da kungiyar Red Cross ta kasar Sin ta samar ga yankunan dake shan fama da tasirin girgizar kasar a kasar Syria a karo na biyu daga birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, kayayyakin da ake sa ran za su taimakawa mutanen dake fama da ibtila’in sama da dubu goma.

Kafin wannan, an riga an mika kayayyakin kiwon lafiya da kungiyar ta samarwa Syria a karo na farko, hannun kungiyar Red Crescent ta kasar, domin amfani da su a yankunan da fama da ibtila’in. (Jamila)