logo

HAUSA

Kasar Sin ta gaggauta tura ma’aikatan ceto zuwa Turkiye da Syria da girgizar kasa ta aukawa

2023-02-11 17:00:48 CMG Hausa

Kasar Sin ta aike da ma’aikatan ceto da muhimman kayayyaki zuwa Turkiye da Syria bayan aukuwar mummunar girgizar kasa a kasashen biyu a ranar Litinin da ta gabata, domin taimakawa wajen bincike da ceton wadanda suka makale cikin baraguzan gine-gine.

Bayan shafe tsawon sa’o’i 3 ana kokari a jiya Juma’a, an ceto wata mace, wadda ta kasance mutum na 4 da ma’aikatan kasar Sin suka ceto, inda suka zakulo ta daga cikin baraguzan gini, bayan ta shafe sama da sa’o’i 96 a makale.

A cewar hukumar raya hadin gwiwar kasa da kasa ta fannin harkokin ci gaba ta kasar Sin (CIDCA), kasar ta Sin ta aike kayayyakin jin kai na farko zuwa Turkiye da safiyar yau Asabar.

Ita ma kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin, ta aike da tawagar ma’aikatan ceto a ranar Alhamis, da kuma kashin farko na kayayyakin kiwon lafiya, domin tallafawa yankin da girgizar ta auku a Syria, wanda kuma yaki ya daidaita.

Haka zalika, da dama daga cikin tawagogin masu ceto na ‘yan sa kai na kasar Sin, sun shiga ayyukan ceto a wuraren.

A cewar hukumar tunkarar iftila’i ta Turkiye, zuwa yammacin jiya Juma’a, adadin wadanda girgizar kasar ta yi sanadin mutuwarsu ya kai 20,213, inda jimilar mamata sanadiyyar iftila’in ya kai sama da 23,000 idan aka hada da na Syria dake makwabtaka da kasar. (Fa’iza Mustapha)