logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira da a gina budadden tsarin raya tattalin arzikin duniya

2023-02-11 16:45:43 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, Dai Bing, ya gabatar da jawabi a wata muhawarar da aka yi a taro na 61 na kwamitin kyautata zaman rayuwar al’umma na majalisar, inda ya yi kira da a aiwatar da tsarin kasancewar bangarori daban-daban, da gina wani budadden tsarin raya tattalin arzikin duniya.

Dai ya ce, duniya na fuskantar manyan sauye-sauye da ba’a taba ganin irinsu ba tsawon shekaru da dama, inda ake bukatar hadin-kan kasa da kasa don shawo kan matsaloli. Dai ya yi kira da a gina wani budadden tsarin bunkasa tattalin arzikin duniya, da samar da kayayyaki ba tare da matsala ba, da adawa da nuna bambancin ra’ayi ga sauran kasashe, ko kuma katse huldar hadin-gwiwar kasa da kasa.

Ya ce ya kamata kasashe masu hannu da shuni su sauke nauyin dake wuyan su, kana, kasashe masu tasowa su zurfafa hadin-kai a tsakaninsu, kuma dukkan bangarorin biyu su hada gwiwa don zama tsintsiya madaurinki daya, da raya huldar abokantaka mai hadin-gwiwa da daidaito da adalci, wadda ke iya samar da alfanu ga kowa da kowa, wato kar a bar kowace kasa da kowane mutum a baya. (Murtala Zhang)