logo

HAUSA

Syria: Saukaka takunkumai da Amurka ta yi ya aike da bahagon sako

2023-02-11 16:54:49 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen Syria ta ce matakin Amurka na baya-bayan nan na saukaka takunkumanta kan kasar domin tallafawa ayyukan jin kai saboda girgizar kasar da ta auku, ya aike da bahagon sako wanda ke da niyyar nuna taimakon jin kai na bogi.

A ranar Alhamis ne ma’aikatar baitulmalin Amurka ta sanar da cewa, za ta dage takunkumai kan Syria na tsawo watanni 6, domin kayayyakin agaji da za a kai kasar, tana mai cewa, takunkuman Amurka kan Syria, ba za su kasance tarnaki ga ayyukan ceton rayuka ba.

A martanin da ta mayar, ma’aikatar harkokin wajen Syria cikin wata sanarwa, ta ce matakin Amurka na ikirarin saukaka takunkumai saboda ayyukan jin kai, amma ba haka gaskiyar batun yake ba.

A cewar ma’aikatar, takunkuman Amurka da manufofinta, sun hana al’ummar Syria samun arziki, inda ta yi kira ga Amurkar ta kawo karshen takunkuman nan take ba tare da wani sharadi ko bata lokaci ba, kuma ta daina aiwatar da muggan abubuwan dake take dokokin kasa da kasa da ka’idoji da manufofin MDD. (Fa’iza Mustapha)