logo

HAUSA

Jami’an aikin ceto na Sin sun taimaka wajen ceto mutum na 3 daga baraguzan gini a Türkiyya

2023-02-10 10:53:49 CMG HAUSA

 

Da karfe 8:00 na daren jiya Alhamis, bisa agogon kasar Türkiyya ne jami’an aikin ceto na Sin da aka tura, tare da takwarorinsu na Turkiyya suka yi nasarar ceto mutum na 3 daga baraguzan ginin da ya danne su, sakamakon mummunar girgizar kasar da ta aukawa wasu sassan kasar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, ma’aikatan sun yi nasarar ceto wata matashiya mai shekaru 20 ko fiye ne daga karkashin wani gini mai hawa 7 da ya rushe. Tun da fari dai jami’an aikin ceton sun gano inda take ne da misalin karfe 5 na yamma, a lokacin tana iya magana sarai. Amma sai bayan sa’o’i 2 suka yi hadin gwiwar zakulo ta daga karkashin ginin, kuma nan take aka garzaya da ita asibiti domin ba ta jinya. (Saminu Alhassan)