logo

HAUSA

Harbo kumbon kasar Sin ya haskaka manufar Amurka

2023-02-10 15:42:40 CMG HAUSA

 

Cikin ’yan kwanakin baya bayan nan, Amurka ta karkata alakar matakan siyasar ga batun kumbon ayyukan farar hula na Sin da ta harbo, bayan da kumbon bisa kuskure ya shiga sararin samaniyar kasar ta. Bayan kwanaki da dama, har yanzu Amurka na ci gaba da baza kalaman zargi kan wannan batu.

Tabbas, wannan lamari ya shaidawa kowa manufar kasar Amurka, tare da zama mizanin fayyacewa duniya mahangar Amurka, game da burin daidaitawa, da inganta alakarta da Sin.

Amurka ta yi amfani da damar fatan da duniya ke da shi, da damuwar da ake nunawa game da alakarta da Sin, ta yadda ta yi amfani da batun kumbon na Sin a matsayin damar dakile Sin, ta kuma nacewa amfani a karfin soji, da aiwatar da matakan wuce gona da iri, wadanda suka yi matukar keta ka’idojin cudanyar kasa da kasa, wanda hakan ya haifar da sabon hadari, da fadada sarkakiyar alakar dake akwai tsakanin sassan biyu.

Wannan kumbo maras matuki, wanda karfin iska ya sauyawa alaka, ya tunzura Amurka daukar matakai marasa dacewa da kyakkyawan tunani, inda ta kai ga yanke hukunci maras adalci. (Saminu Alhassan)