logo

HAUSA

Adadin wadanda girgizar kasar Turkiyya ta hallaka ya karu zuwa sama da mutum 20,000

2023-02-10 11:08:14 CMG HAUSA

 

Rahotanni na cewa tsananin sanyi, da yunwa, da fargabar karuwar mamata sakamakon mummunar girgizar kasa da ta aukawa kudancin Turkiyya da makwafciyarta Syria kwanaki 3 da suka gabata, sun jefa dubban al’ummun kasashen 2 cikin mummunan yanayi.

Baya ga gawawwakin da ake zakulowa daga baraguzan gine-ginen da suka rushe, dubban al’ummu sun rasa matsugunan su. Ya zuwa jiya Alhamis, an tabbatar da rasuwar mutane sama da 20,000.

Nasarar da aka samu ta ceto wani yaro karami dan shekaru 2, bayan shafe sa’o’i 79 yana karkashin baraguzan gini a garin Hatay na Türkiye, da ma karin wasu mutane da dama da aka ceto, ya karfafa gwiwar masu aikin ceto. To sai dai kuma a halin yanzu, an fara yanke tsammanin gano karin mutane da ran su, daga garuruwa da biranen da ibtila’in ya shafa.

Adadin wadanda girgizar kasar ta kwanan nan ta hallaka dai ya haura mutum 17,000, wanda makamanciyarta ta shekarar 1999 ta haddasa a arewa maso yammacin Türkiyya. (Saminu Alhassan)