logo

HAUSA

Sin: A dora karin muhimmanci kan aikin raya kasashe daban daban

2023-02-09 11:13:33 CMG Hausa

Mataimakin wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya Dai Bing, ya bayyana a jiya Laraba cewa, kamata ya yi gamayyar kasa da kasa, su rungumi ra’ayin baiwa karin bangarorin duniya damar fada a ji, da daukaka matsayin MDD, gami da dora karin muhimmanci kan aikin raya kasashe daban daban.

Dai ya fadi haka ne yayin da yake halartar wani taron majalissar raya tattalin arziki da al’umma ta MDD, inda ya yi kira da a kare hakkin kasashe masu tasowa na neman raya kai, da kokarin biyan bukatunsu a fannonin rage talauci, da samar da abinci, da dakile yaduwar cututtuka, da kare muhalli, da tsimin makamashi, da sauya fasalin tattalin arziki, da dai makamantansu.

Jami’in na kasar Sin ya kara da cewa, ya kamata kasashe masu sukuni su cika alkawarin da suka yi, na taimakawa raya kasashe masu tasowa, da zuba kudi ga hukumomin MDD masu kula da raya al’ummun kasa da kasa. Ya ce, kasar Sin na adawa da ra’ayin daukar matakan kashin kai, da kariyar ciniki. Haka kuma tana goyon bayan kasashe masu raunin karfin tattalin arziki, ta yadda za su yi amfani da tallafin da aka ba su wajen neman dabarun raya kansu, tare da samun ci gaba mai dorewa. (Bello Wang)