logo

HAUSA

Tawagar Sin ta taimaka a ayyukan ceto dake gudana a Hatay na kasar Türkiyya

2023-02-09 10:59:33 CMG HAUSA

 

Tawagar jami’an aikin ceto ta kasar Sin, da hadin gwiwar takwarorinsu na kasar Türkiyya, sun ceto wata mata mai ciki daga karkashin baraguzan gini mai hawa 8 da ya rubza.

Jami’an sun yi nasarar ceto matar ne da sanyin safiyar yau Alhamis, bayan aukuwar mummunar girgizar kasa da ta lalata gine gine da dama a ranar Litinin.   (Saminu Alhassan)