logo

HAUSA

Shugaban Iran ya sa hannu kan dokar amincewa da shigowar kasarsa kungiyar SCO

2023-02-08 10:05:08 CMG Hausa

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, ya sa hannu kan dokar amincewa da shigar kasarsa kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO jiya Talata.

Bisa sanarwar da aka fitar a shafin internet na shugaban kasar, shugaba Raisi ya mika dokar amincewar ga ma’aikatar harkokin waje don aiwatar da ita. Sanarwar ta bayyana cewa, kungiyar SCO ta gudanar da ayyuka da dama a fannin raya tattalin arziki da sauransu, bayan da kasar Iran ta shiga kungiyar, za ta kara tabbatar da moriyarta a fannoni masu alaka.

Kaza lika, daya daga cikin ma’anar shigar Iran kungiyar ta SCO shi ne sa kaimi ga kasar Iran, wajen shiga shawarar “ziri daya da hanya daya”.

A gun taron karo na 22, na majalisar shugabannin kasashen membobin kungiyar SCO da aka gudanar a watan Satumba na shekarar 2022, an daddale takardar fahimtar juna, game da shigar da kasar Iran cikin kungiyar ta SCO.

A ranar 27 ga watan Nuwanba na shekarar 2022, majalisar dokokin kasar Iran ta zartas da daftarin dokar shigar kasar kungiyar SCO. Kana a ranar 28 ga watan Janairu na bana, kwamitin sa ido kan kundin tsarin mulkin kasar Iran ya bayar da labarin cewa, kwamitin ya riga ya amince da wannan daftarin doka. (Zainab)